Saudiyya domin kare kansu daga faɗawa hali mara daɗi a ƙasa mai tsarki

0
390

Sakataren ƙungiyar na shiyyar Arewa, Alhaji Muhammad Hadi Salisu ne ya yi wannan jan hankalin ta cikin hirar da tashar Freedom Radio, Kaduna ta yi da shi ta wayar tarho.

Bayan yaba wa rawar da Hukumar Aikin Hajji ta Kasa, NAHCON, ke takawa wajen kula da harkokin Hajji a Najeriya, Salisu ya kuma sha alwashin ƙungiyarsu za ta bai wa maniyyatan hidima.imgantacciya a yayin aikin Hajji.

Ya ce, mambobin ƙungiyar sun yi kyakkyawan shiri a Saudiyya domin tabbatar da maniyyata sun gudanar da aikin Hajjin na bana cikin kwanciyar hankali da walwala.

Daga nan, ya shawarci maniyyatan da su zamanto jakadu nagari ga Musulunci da ma al’ummar Musulmin Najeriya a yayin zamansu a ƙasa mai tsarki ta hanyar kiyayewa da kuma martaba dokokin ƙasar.

A ƙarshe, Alhaji Hadi ya nuna farin cikinsa dangane da haɗin kan da hukumar NAHCON kan bai wa ƙungiyar da mambobinta a inda ya dace.