Gwamnan Kano ya rusa shugabancin hukumar akhazai tare da nada sabbin shugabanni

0
519

Sabon Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Shugaba, Sakataren Gudanarwa da kuma mambobin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano.

Sanarwar da Gwamnatin Jihar ta fitar mai ɗauke da sa-hannun Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamna, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ta nuna waɗanda naɗin ya shafa su ne, Alhaji Yusuf Lawan a matsayin sabon Shugaban hukumar da Alhaji Laminu Rabi’u kuma tsohon sakataren hukumar a matsayin sabon Sakataren ta.

Sai kuma Sheikh Abbas Abubakar Daneji, Shiek Shehi Shehi Maihula, Ambasads Munir Lawan- Member, Shiek Isma’il Mangu, Hajiya Aishatu Munir Matawalle da Dr. Sani Ashir a matsayin mambobin hukumar.

Sanarwar ta ce, “Sabbin masu mukaman za su karɓi ragamar gudanarwar da hukumar nan take domin tabbatar aikin Hajjin 2023 ya cimma nasara.”