Hajjin bana: Rukunin farko na alhazan jihar Bauchi ya tashi zuwa Saudiyya

0
445

Rukunin farko na maniyyatan Jihar Bauchi da ya ƙunshi mutane 528, sun tashi zuwa ƙasa mai tsarki a jirgin MaxAir VM1005, inda ya bar Babban Filin Jirgin Sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi da misalin ƙarfe 3:16 na subahin yau Talata, 30 ga Mayu, 2030.

Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya bayyana farin cikinsa ganin an fara jigilar maniyyatan jihar cikin nasara.

Kakakin hukumar, Muhammad Sani Yunusa, shi ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai gabanin tashin jirgin, inda ya ce shirin jigilar maniyyatan ya kankama cikin nasara.

Ya ce, rukunin na farkon ya ƙunshi maniyyata daga ƙananan hukumomin Ningi da Ganjuwa da kuma waɗanda suka shiga shirin adashin gata na zuwa Hajji.

Sakataren ya ce maniyyatan sun nuna halin ya kamata, lamarin da ya ce ya kamata takwarorinsu su yi koyi da su.

Daga nan, ya miƙa godiyarsa ga Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, dangane da gudunmawar da yake ba wa hukumar, yana mai cewa hukumar ba za ta gajiya ba wajen ci gaba da nuna godiya ga Gwamnan bisa tallafinsa gare ta