Hajjin 2023: NAHCON ga Mahajjata: Kada ku tallafa wa masu siyar da abinci a Saudiyya.

0
269

Hajjin bana: Ku guji sayen abinci a wajen da ba hukumomi ba su amince da shi ba

Hukumar alhazai ta ƙasa, NAHCON, ta gargadi maniyyata da su guji sayen abinci a wajen da ba a amince da shi ba.

Ko’odinetan hukumar a Madina, Alhaji Ibrahim Mahmud ne ya yi wannan gargadin a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa, (NAN) a yau Laraba a Madina.

Mahmud ya ce hukumar ta kulla yarjejeniya da wasu zaɓaɓɓun masu sayar da abinci da ta amince da su don ciyar da alhazai domin kare su daga gurbataccen abinci.

Ya yi bayanin cewa NAHCON ta ta kulla yarjejeniya da kamfanonin sayar da abinci da ke kasar Saudiyya tare da hadin gwiwar masu sayar da abincin ‘yan asalin Najeriya domin shirya abincin gida ga mahajjata.

Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu hukumar ta duba dakunan dafa abinci inda masu ba da abinci za su rika tanadar wa alhazai abinci domin tabbatar da cewa maniyyatan sun samu kimar kudinsu.