Masu ruwa da tsaki na yabawa NAHCON kan nasarar fara shirye-shiryen aikin Hajjin bana

0
315

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, na ci gaba da shan yabo daga masu ruwa da tsaki dangane da shirye-shiryen aikin Hajji na bana.

Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Kaduna, Dr. Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ne ya bayyana haka yayin wani shiri da aka yi da shi mai taken: “Barka Da Warhaka”, a tashar Freedom Radio Kaduna.

Ya ce Shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan tare da masu ruwa da tsaki sun yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ba a tsawwala wa maniyata kuɗin Hajji ba.

Ya ƙara da cewa, maniyyatan na bana sun fuskanci ƙarin kuɗin Hajji ne saboda tsadar masauki, kuɗin mota da sauransu a ƙasa mai tsarki da kuma faɗuwar darajar Naira a kan Dala.

Dr. Yusuf Arrigasiyyu ya ce yana da tabbacin za a kammala jigilar maniyyatan Jihar Kaduna zuwa Saudiyya kafin 14 ga Yuni, tare da cewa an gaza fara jigilar maniyyatan a kan kari ne saboda wasu ‘yan ƙalubalan da aka fuskanta.

A cewarsa, kamfanin jirgin Azman Air wanda nauyin jigilar maniyyatan ya rataya a wuyansa, shi ne ya tsaya gyare-gyaren wasu ‘yan matsaloli da ya gano, ya ce ya zuwa ranar Alhamis ko Juma’a za a fara jigilar maniyyatan.

Daga nan, ya shawarci maniyyatan da su kame kamsu yayin zamansu a ƙasa mai tsarki kanscewar canjin yanayi na bana ya bambanta da na bara.