Hajj 2023: Azman zai fara jigilar maniyyata a yau

0
694

Azman Air, ɗaya daga cikin jiragen sama guda biyar da aka zaba domin jigilar alhazan Najeriya zuwa aikin Hajjin bana zai fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a yau Alhamis.

Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta baiwa Azman Air kujeru 8660 na maniyyata.

Wani jami’in kamfanin ya sanar da HAJJ REPORTERS ta wayar tarho cewa, a karshe dai kamfanin ya warware duk wata matsala da ta shafi takardu daga kasa mai tsarki, kuma zai fara aiki a yau.

“Za mu fara da Jigawa a yau, sannan mu wuce zuwa wasu wurare. Mu na fatan yin jigilar alhazai cikin nasara ba tare da matsala ba kuma mu na da kwarin gwiwar jigilar dukkan fasinjojinmu zuwa kasa mai tsarki a kan lokaci,” inji shi.