Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Yobe, ta ba da sanarwar cewa ya zuwa ranar Asabar, 3 ga Yuni, 2023 za a fara jigilar maniyyatan jihar.
Sakataren Hukumar, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ne ya sanar da hakan a lokacin da yake yi wa maniyyata da jami’ai jawabi.
Sanarwar da Ofishin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Suleiman Alhaji Sabo, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce Shugaban hukumar ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga jami’an hukumar da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu tare da yaba musu bisa ƙoƙarin da suke yi
Kazalika, Alhaji Biriri ya jaddada wa ma’aikatan su sani cewa sai da haɗin kai ake iya cimma nasara a bakin aiki.