
Allah Ya yi wa maniyyaciya daga Jihar Yobe, Fanna Hassan, rasuwa a Sansanin Alhazai da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Jami’in alhazai na shiyya na Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), mai kula da shiyyar Maiduguri, Alhaji Wali Gana ne ya shaida wa HAJJ REPORTERS rasuwar marigayiyar da safiyar Asabar.
A cewar jami’in, marigayiyar na ɗaya daga cikin rukunin farko na maniyyatan Jihar Borno da aka tsara yin jigilarsu zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya ƙara da cewa, “An shirya jirginsu zai tashi da misalin ƙarfe 11:00 na safe wanda shi ne rukunin farko na maniyyatan Jihar Yobe amma sai Allah Ya yi mata cikawa bayan sallar asuba a sansanin, ikon Allah ke nan.”
Da fatan Allah Maɗaukaki Ya gafarta kura-kuranta, kana Ya sanya ta a Aljanna Firdausi, amin.