Gwamnatin Kano ta sauke jami’an alhazai na kananan kukumomi 44 tare da maye gurbin su da na wucin-gadi

0
518

Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da sauke jami’ai masu kula da alhazai a kananan hukumomi 44 na jihar, tare da nada jami’an riko da za su gudanar da jigilar maniyyata aikin hajjin 2023 da ke gudana a fadin jihar.

A wata sanarwa da aka fitar da safiyar Lahadi mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban sakataren yada labaran gwamnan, ya umurci jami’an aikin hajjin na rikon kwarya da su karbe ragamar aiki daga waɗanda aka sauke.

Bayan haka, sanarwar ta umurci sabbin jami’an cibiyar da aka nada da su garzaya zuwa ga sabon Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano a yau Lahadi, 4 ga watan Yuni, 2023 don wani taron gaggawa a hedikwatar hukumar.

HAJJ REPORTERS ta tattaro cewa amincewa da sabbin jami’an wucin gadi, wadanda dukkan su yan Kwankwasiyya ne, ya zo ne a lokacin da jami’an alhazan da aka sauke sun kammala duk wani shirye-shirye na aikin Hajjin bana.

A tuna cewa sabuwar gwamnati ta maye gurbin Ambasada Mohammad Abba Danbatta, da Alh. Laminu Rabiu a matsayin Darakta Janar na hukumar.

Wannan sauyi na jami’an alhazai ya gudana ne kasa da ‘yan sa’o’i kafin fara jigilar Alhazan Jihar Kano da aka shirya farawa a yau 4 ga watan Yuni.

Tun da fari, HAJJ REPORTERS ta shawarci gwamnonin jihohi masu jiran gado da kada su canza tsare-tsaren da jami’an alhazai su ka gudanar a bana.