Kwamitin Malamai na Hukumar Hajji ta Najeriya, NAHCON, ya gargaɗi maniyyata da su guji zirga-zirga a cikin rana yayin da suka isa Saudiyya, yana mai cewa za a fuskanci zafin rana mai tsanani yayin Hajjin bana kamar yadda jaridar Muslim News ta ruwaito.
Malaman sun yi gargaɗin ne yayin taron da suka yi da tawagar NAHCON ƙarƙashin jagorancin Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan a Hajj House da ke Abuja ranar Laraba, 31 ga Mayu, 2023.
Babban limamin rukunin gidaje na Prince and Princess da ke Abuja, Imam Tajudeen Oyebanji, ya yaba wa shugabancin NAHCON bisa ƙoƙarin da take yi wajen tabbatar da an cimma nasara a Hajjin bana, sun ce malamai zai su zage dantse wajen faɗakar da ɗaukacin maniyyatan Najeriya.
Imam Oyebanji wanda ya kasance kodinetan JIBWIN na yankin Kudancin Najeriya, ya ce binciken malaman ya gano za a yi fama da tsananin zafin rana a Hajjin na bana, tare da kira ga maniyyatan da su zama masu kulawa kana su guji yawo a cikin rana.
“Mafi muhimmanci shi ne kada su bar tantunansu yayin zamansu a Muna ko ɗakunansu na otel a Makkah sai dai in ya kama dole. Idan ya kama babu makawa sai an fita, a yi amfani da lema kuma a guji tafiya babu takalmi don kare kai daga zafin rana,” in ji shi.