Yau za a fara jigilar alhazai a jihar Kano

0
754

Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta shirya fara jigilar maniyyatan jihar zuwa Saudiyya don gabatar da Hajjin 2023.

Cikin sanarwar da ta fitar ta Sashen Hulɗa da Jama’a, Hukumar ta buƙaci maniyyata daga yankunan Tudun wada, Doguwa, Bebeji da Garun Malamda su hallara a sansanin alhazan jihar yau Lahadi da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

Hukumar ta kuma buƙaci maniyyatan da su kasance sanye da tufafi na bai-ɗaya da aka tanadar musu domin jigilarsu zuwa ƙasa mai tsarki.