Za mu kammala jigilar alhazan da aka ware mana a kan lokaci — Azman Air

0
778

Kamfanin jirgin sama na Azman Airline, ya sha alwashin kammala jigilar maniyyatan Najeriya da aka ƙayyade masa zuwa ƙasa mai tsarki a kan kari.

Azman Airline na daga cikin kamfanoni biyar da Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON, ta naɗa domin kwashe maniyyatan ƙasar zuwa Saudiyya don Hajjin bana.

Babban Manajan kamfanin, Engr. Nuruddeen Aliyu, shi ne ya bayyana hakan a wata hira da tawagar yaɗa labarai ta NAHCON ta yi da shi ta wayar salula a Kaduna.

Aliyu ya ce, duk da kamfanin ya fuskaci ‘yar matsala daga ɓangaren Saudiyya a watan jiya, wannan ba zai hana shi sauke nauyin da ya rataya a kansa ba, musamman duba da za a samu ƙarin jirgi ya zuwa makon gobe domin aikin jigilar, don haka ya ce jiragensu za su riƙa tashi da maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki kulli yaumi.

Jami’in ya bayyana gamsuwarsa da halin da Hukumar Alhazai ta Kaduna da ma maniyyatan jihar suka nuna, sannan ya yaba wa NAHCON kan irin tanade-tanaden da ta yi domin tabbatar da aikin Hajjin na bana ya gudana cikin aminci da kwanciyar hakali.

Kawo yanzu dai kamfanon ya kammala duk wani shiri domin kwashe maniyyatan Jihar Kaduna rukuni na biyu a ranar Litinin (yau).

Maniyyatan da kamfanin Azman Airline zai yi jigilarsu zuwa Saudiyya sun haɗa da na Jigawa (wanda ake kyautata zaton ya kammala), Jihar Kaduna da kuma tawagar jami’an tsaro.