Hajjin bana: NAHCON ta samar da wani tsari na zaman Madina ga alhazan Nijeriya

0
595

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta samar da wasu sabbin dokoki waɗanda za su bai wa alhazai damar barin Madina zuwa Makka bayan kwana 5, kuma tuni dokokin suka fara aiki a ranar Talata, 8 ga Yuni, 2023.

NAHCON ta ce an samar da dokokin ne biyo bayan ƙorafin da aka samu game da cunkoson maniyyatan Nijeriya a birnin Madina.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na NAHCON, Mousa Ubandawaki, ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce wannan shi ne karon farko da NAHCON ta bai wa maniyyatan Nijeriya dama ɗari bisa ɗari na ziyartar Madina kafin Arafat.

Ta ƙara da cewa, domin cimma hakan da kuma kauce wa fuskantar takunkumi idan aka samu cunkoso maniyyata a Madina, hakan ya sa hukumar ta samar da sabbin dokokin bayan tattaunawa da kuma shawarwari.

Bugu da ƙari, jami’in ya ce sanannen abu ne cewa maniyyatan Nijeriya na zama ne a keɓaɓɓen wuri, Markaziyya, yayin zamansu a Madina wanda hakan ya haifar wa NAHCON yabo.

Sai dai kuma, ya ce muddin ana so a ci gaba da samun wannan dama, ya zama wajibi a rage adadin kwanakin da maniyyatan za su riƙa yi a Madina.

Haka nan y ce, a bayyane yake cewa ana samun sauye-sauye a yanayin ayyukan Hajji da cigaba tabbatacce, muddin NAHCON na son cimma manufofinta na Hajjin 2023 na tabbatar da komai ya gudana kamar yadda aka tsara, dole a daidaita batun jigilar maniyyata zuwa Ƙasa Mai Tsarki.