Hukumar Alhazai ta Jihar Adamawa ta samu nasarar kammala jigilar maniyyatan jihar zuwa Saudiyya don aikin Hajjin 2023.
Jirgin da ya kwashi rukunin ƙarshe na maniyyatan, wato Aero Flight, mai lamba NIG9033 ya bar Babban Filin Jirgin Saman Lamido Aliyu Mustapha da ke jihar da misalin ƙarfe 10:19 na dare na ranar Juma’a ɗauke da maniyyata 217.
Maniyyatan jihar sun bayyana farin ciki da gamsuwarsu game da nasarar da hukumar ta samu ƙarƙashin jagorancin Sakataren Hukumar, Malam Abubakar Salihu.
Malam Abubakar Salihu ya yi kira ga ɗaukacin maniyyatan jihar da su kasance masu karrama juna da kuma yi wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri addu’ar samun nasara game da jagorancin jihar.
Kazalika, Babban Sakataren Hukumar da ma Sakataren Zartarwarta, baki ɗaya sun nuna godiyarsu ga Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, bisa goyon bayan da yake bai wa Hukumar wanda hakan yake ba ta zarafin sauke nauyin da ya rataya a kanta yadda ya kamata.