Babu maniyyacin da zai rasa aikin Hajji na bana – NAHCON

0
376

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta jaddada aniyyarta ta kwashe duka maniyyatan bana zuwa Saudiyya ya zuwa wa’adin da aka ƙayyade a hukumance.

Kwamishina a NAHCON, Sheik Suleiman Imonikhe Momoh ne ya bayyana haka a Hedikwatar Hukumar da ke Abuja.

Sheik Mohmoh ya yi ƙarin haske kan nasarorin da hukumar ta samu dangne da jigilar maniyyata daga Nijeriya zuwa Saudiyya tun bayan da shirin jigilar ya kankama.

A cewarsa; “Sama da maniyyata 67,000 daga cikin 73,000 da ake da su, aka samu nasarar kwashe su zuwa ƙasa mai tsarki inda ake sa ran jigilar kafin 24 ga Yuni.

“Maniyyata 6000 da suka rage za a kwashe su kafin ranar da za a rufe filin jirgin saman Saudiyya, 24 ga Yuni,” in ji jami’in.

Kazalika ya ce, “Hukumar ta samar da wadataccen tsaro, ingantaccen tsarin kiwon lafiya da sauran muhimman ayyuka ga maniyyatan yayin zamansu a Saudiyya.”