A yau ne kwamitin kula da hadaya na alhazan jihar Katsina ya kammala yi wa alhazan hadayar su ta aikin Hajji.
Hadaya shi ne yanka dabba da mahajjata ke yi kamar yadda addini ya koyar, kuma rukuni ne da ga cikin rukunnan aikin Hajji.
Wata gajeriyar sanarwa daga hukumar jin dadin alhazai ta Katsina ta ce kwamitin hadayar ne ya je mayankar bayan sallar Azahar a yau Juma’a, inda ta kara da cewa sun sami nasarar kammala yi wa Alhazan hadayar su lami lafiya.