Ofishin Jakadncin ƙasar Philippines ya bayyana cewa, an yi nasarar kwashe mahajjatan ƙasar su sama da 200 da suka maƙale a Mina saboda rashin wadatar tanti zuwa Makka.
A cewar ofishin a Riyadh, ‘yan Philippine 7,200 ne aka yi jigilarsu zuwa Hajjin bana. Ya ƙara da cewa mutum 10 daga cikin 200 da suka maƙale ɗin, sun yi fama da rashin lafiya Mina kuma an yi musu magani har an sallame su.
Wannan na zuwa ne bayan da rahotanni daga ƙasa mai tsarki suka nuna mahajjata sun fuskanci zafin rana mai tsanani yayin aikin Hajji a Makka.
Ofishin ya ƙara da cewa, babu wani alhajin Filippine da ya fuskanci rashin lafiya mai tsanani. Ya ce mutum 10 da aka kai asibiti an sallame su ba da jimawa ba tare da maida su Mina ba tare da wata matsala ba.
Haka nan, ofishin ya ce mahajjatan ƙasar su 7,200 ne suka haɗu da takwarorinsu sama da mutum 1.8 wajen sauke faralin bana a Saudiyya.
Jami’an Saudiyya sun bayyana cewa, mahajjata sama da 2,000 ne suka gayyara saboda matsanancin zafin rana a yayin aikin Hajji.
An kuma ga mahajjata tsofaffi da daman gaske a Hajjin na bana sakamakon shafe dokar nan ta Korona da ta ƙayyade shekarun zuwa Hajji a 2021.
Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya ta ce, ɗaruruwan mahajjata aka yi wa maganin matsaloli masu nasaba da zafin rana mai tsanani, ciki har da wani dattijo mai shekara 78 daga Filippine wanda aka yi nasarar yi masa aiki a zuciya a Makka.
Yayin da masu ibada da ke tururuwa zuwa aikin Hajji a baya suka yi ta fama da haɗarin fuskantar tarzoma da hare-haren ‘yan bindiga, bana dai babban ƙalubalen ya zo ne daga matsanancin zafi.