Hajjin bana: Ambasadan Nijeriya a Saudiyya ya ziyarci alhazan Katsina a Makkah

0
160

Ambasadan Nijeriya a Saudi Arebiya, Alhaji Lawal Rafin-dadi ya kai wa alhazai da jami’an su na jihar Katsina a ranar Alhamis a Nuna, Makkah.

Ambasadan, Wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin jami’an Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ga guda nar da ddu’oin neman kariya ga ƙasa Nijeriya da jihohi da shugabanni da sauran al’ummah baki daya.

Ya yi fatan alheri ga dukkan alhazan jihar Katsina da kuma yi masu murnar kammala aikin Hajji su cikin koshin lafiya.

Wadanda su ka tarbi ambassadon sun hada da Amirul Hajji na jihar Katsina, Hon.Tasiu Maigari Zango, Shugaban Majalisar Dokoki ta Katsina, Hon.Nasiru Yahaya Daura, Babban Daraktan Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Katsina, Alh.Suleiman Nuhu Kuki da sauran masu ruwa da tsaki akan aikin Hajji na jihar.