Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta bayyana cewa Najeriya ta yi rashin maniyyata 14 a kasar Saudiyya daga fara gudanar da aikin hajjin 2023 zuwa yanzu.
Shugaban tawogar likitoci ta NAHCON, Usman Galadima ne ya bayyana haka a wani taron bayan Arafat da masu ruwa da tsaki a jiya Lahadi a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Galadima ya bayyana cewa mahajjata bakwai sun rasu kafin Arafat, inda wasu guda shida kuma su ka rasu a cikin kwanaki biyar na Mashair (babban lokacin Hajji da ake yin zaman Mina) sannan karin mutum daya ya rasu bayan Arafat.
“Mun sami rahoton mutuwar mutane shida a Mashair, hudu sun mutu a Arafat, sauran biyun kuma sun mutu a Mina.
“Tun da fari, mun rasa mahajjata bakwai kafin Arafat kuma a yanzu haka an sanar da ni cewa mun rasa wani alhaji. Wannan ya kawo adadin wadanda suka rasu zuwa 14.
“Yawan mace-mace yayi kama da na 2019,” in ji shi.