Hukumar Kula da Yanayi ta Kasar Saudiyya ta sanar da cewa yanayin zafi a gobe Jumma’a, 8/7/2023 zai kai daraja 50° na tsananin Zafi.
Saboda wannan zafin yanayin, Gwamnatin Saudiyya na bada shawarar cewa Alhazai da suyi Sallar Jumma’ah a Masallatan da suka fi kusa da gidajensu, ba sai sun je Harami ba, don kaucewa shiga tsananin rana.
Don haka Ma’aikatar Aikin Hajji ta Kasar Najeriya ta yi kira ga alhazan ƙasar da su yi amfani da wannan shawara ta yin Salla a Masallatai Mafi kusa da Masaukan su.
Kamar yadda sanarwa daga Dr. Ibråhìm Muhammad Sodangi, Babban Jami’in Hukumar Alhazai ta Kasa a Birnin Makkah ta bayyana a yau Alhamis.