Alhazai 1,670 daga jihar Kano ya zuwa yanzu sun sauka a filin jirgin sama na Aminu Kano bayan gudanar da aikin hajjin 2023 a kasar Saudiyya.
Alhazan sun isa gida ne a sahu uku na jirgi, da su ka hada da alhazai 560 da suka iso ranar Litinin da karfe 9:56 na dare, da suka hada da Alhazai daga kananan hukumomin Albasu da Garko da kuma Ungoggo.
Sauran rukunin sun bar filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz na Jeddah a ranar Talata tare da mahajjata 538 da jami’ai 14.
A wata hira da manema labarai, daraktan ayyuka na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Alhaji Kabiru Muhammad Panda ya ce kawo yanzu hukumar ta kwaso alhazai daga kananan hukumomin Tudunwada, Doguwa, Garun Malam, Bebeji, Albasu da Garko.
Ya yabawa Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON bisa nuna rashin amincewarsu da matakin da hukumomin Saudiyya suka dauka tun da farko na jigilar tawagar Kano daga Madina a maimakon Jeddah.