Ƴan ƙasar Bangladesh 114 ne suka rasu a yayin aikin Hajjin bana a Saudi Arebiya.
Rasuwar baya-bayan nan ita ce ta wani Matiur Rahman a ranar Asabar.
Daga cikin 114 da suka mutu, 89 maza ne, 25 kuma mata ne, inda 94 daga cikinsu sun rasu a Makka, bakwai a Madina, ɗaya a Jeddah, tara a Mina, biyu a dutsen Arafa, daya kuma a Muzdalifah.
Alhazan Bangladesh 88,418 ne su ka dawo gida ya zuwa ranar Asabar bayan kammala aikin Hajjin na bana.
A bana sama da mutum miliyan 1.8 ne su ka gudanar da aikin hajji, wanda daya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kuma yana cikin manyan tarukan addini na duniya.
Sama da mutane 2,000 ne suka fuskanci larurori daban-daban sakamakon matsanancin yanayin zafi a bana, a cewar hukumomin Saudiyya, bayan da yanayin zafi ya kai ma’aunin Celsius 48.
Ainihin adadin waɗanda suka kamu da rashin lafiya sakamakon zafi- wanda ya haɗa da zafin jiki, gajiya, ciwon ciki da ƙuraje – tabbas ya fi yadda ake tsammani saboda yawancin marasa lafiya ba a kai su a asibiti ba.
Alkaluman mahajjata na bana sun nuna karuwar 926,000 a kan bara, lokacin da adadin ya kai miliyan daya sakamakon cutar ta Covid-19.