Hajjin bana: Wata Hajiya yar Jihar Neja ta rasu a Makkah

0
114

Allah Ya yi wa wata hajiya daga Jihar Neja mai suna A’isha Alhassan, rasuwa a Saudiyya.

Hadimar Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Neja kan sha’anin yaɗa labarai, Hassana Isah, ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar a yau Talata cewa, marigayiyar, ƴar asalin Ƙaramar Hukumar Mokwa ta rasu ne a jiya Litinin a Asibitin Sarki Faiz da ke Makkah.

A cewar Aisha, marigayiyar ta rasu ne bayan fama da matsananciyar cuta da ta shafi wasu sassan jikinta na tsawon lokaci.

Ta ƙara da cewa, an sallaci marigayiyar a Masallacin Harami na Makkah da sanyin safiyar yau Talata.

“Mahalarta jana’izar sun haɗa da Daraktan Ayyuka na Hukumar Alhazan Jihar, Alh Attahiru Bala Dukku, ɗanta da kuma ɗan uwanta da sauran jami’ai.