Ma’aikatar Hajji da Umrah ta hana yin barci a Harami

0
151

Ma’aikatar Hajji da Umarah ta ƙasar Saudiyya ta yi kira ga alhazan ummara da sauran baƙi masu zuwa ibada da su daina yin barci a Masallacin Harami da ke Makka don kiyaye sharuɗɗan da aka gindaya.

Ma’aikatar ta ce alhazan Ummara su guji yin barci ko kwanciya musamman a harabar masallacin da wuraren sallah da hanyoyin da aka keɓe don masu zama a kekem guragu saboda masu rauni ko nakasa.

Kazalika, Ma’aikatar ta ce wajibi ne alhazan Ummara su kiyaye dokokin Umarah da suka haɗa da wanzar da kyakkyawar mu’amala tare da bin ƙa’idojin da ma’aikata suka gindaya.

Ta ƙara da cewa, domin kauce wa saɓa dokoki, duk mai son yin Umarah tilas ya mallaki takardar izinin (permit) da za ta ba shi zarafin haka kafin isa Masallacin Ka’aba da ke Makkah.

Ta ce, za a iya nemanizini (permit) ta amfani da manhajar Nusuk ko ta Tawakkalna a yanar gizo.