Sharararren ɗan wasan gaban Senegal, Sadio Mane ya yi Umrah tare da abokan taka ledar sa na sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafar da ya koma, Al-Nassr da ke Saudi Arebiya.
Mane, mai shekaru 31, ya sauya sheka ne zuwa Al-Nassr bayan ya shafe kaka daga take a Bayern Munich ta kasar Jamus.
Bayan Al-Nassr ta yi 1-1 da Zamalek a wasan cin kofin zakarun ƙasashen larabawa, sai Mane da shi da abokan wasan sa, su ka dunguma zuwa Makkah domin gudanar da ibadar Umrah.