Hukumar alhazai ta Kaduna ta buƙaci maniyyata da su ajiye N3.5m kuɗin Hajjin 2024

0
456

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, Dakta Yusuf Alrigasiyyu ya buƙaci maniyyata da ke son zuwa Hajjin badi na 2024 da su ajiye Naira miliyan 3.5 na kujerar Hajji.

Hukumar ta kuma sanya ranar 1 ga Satumba, 2023, a matsayin ranar da za a fara karbar kudaden ajiya daga hannun maniyyatan jihar.

Za a gudanar da wadannan kudaden ne har zuwa lokacin da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ƙayyade kudin da za a biya na karshe na aikin Hajji badi.

Daily Trust ta rawaito cewa ya bayyana hakan ne a jiya Laraba lokacin da ya bayyana a gidan rediyon Freedom radio a Kaduna don bayar da karin haske kan aikin hajjin 2023.

“Daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa zuwa Disamba, za mu karbi kudaden kudin aikin Hajji daga masu niyyar zuwa aikin Hajji. Muna sa ran kowane maniyyaci zai saka akalla Naira miliyan 3.5, inda hukumar NAHCON za ta bayyana kudin da za ta biya,” Dr. Alrigasiyyu ya bayyana.

Ya kuma kara da cewa manufarsu ita ce kudin aikin Hajji ya gaza Naira miliyan 3.5, wanda hakan zai sa a mayarwa da maniyyata rarar kudadensu da suka ajiye Naira miliyan 3.5.

Dokta Alrigasiyyu ya nuna damuwarsa kan yadda tsofaffin alhazai su ka halarci aikin Hajjin 2023, duk da gargadin da hukumar ta yi.

Ya yi nuni da cewa wasu tsofaffin alhazai sun dogara ga jami’an aikin Hajji don kula da su a Saudiyya saboda yawan shekarun su.

Da yake bayar da gargadin, ya bayyana cewa daga shekara mai zuwa, za a ba wa tsofaffin alhazai damar ziyartar kasa mai tsarki ne kawai idan da wani wanda za su kula da su.