Hukumar alhazai ta Kano ta bada tallafin abinci da kuɗi ga iyalan alhazanta 2 da su ka rasu a Saudiyya

0
464

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wasu alhazai da suka rasu a kasa mai sarki yayin gudanar da aikin hajjin bana.

Babban daraktan hukumar, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa shi ne ya jagoranci tawagar daraktoci hukumar domin zuwa taaziyar.

Tawagar ta fara ziyartar kauyen Gago Rikadawa dake karamar hukumar Madobi inda aka yiwa iyalam Hajiya Hadiza Ismail ta’aziyya , bayan nan aka gabatar musu da kayan abinci da kudi wanda hukumar ta bayan ga iyalan marigayiyar.

A jawabin shugaban hukumar Alh. Laminu Rabi’u, yace marigayiyar ta rasu a birnin Makka kuma anyi mata sallah a masallacin Harami, sannan yayin musu ta’aziyya tare da yiwa mamaciyar addu’o’in samun rahamar Allah (S W A).

Daga bisani tawagar ta kai ziyara garin Rimin Gado domin yin ta’aziyya ga iyalan mai unguwa Dan Azumi mai unguwar Zangon Dan Audu dake Rimin Gado wanda shi ma Allah ya karbi ransa a kasa mai sarki bayan gajeriyar jinya da yayi fama da ita, inda anan ma aka gabatar a addu’a ga mamacin sannan aka mika musu abinci da kudi.

Sannan tawagar ta kai ta’aziyya ga iyalan margayi, Alhaji Shitu Inuwa Gunduwawa da ke karamar hukumar Gezawa wanda Allah ya karbi ransa a kasa mai tsarki , bayan ya kammala aikin hajjinsa, Babban daraktan hukumar jindadi alhazai ta jihar kano , Alh. Laminu Rabiu Dan bappa ya gabatarwa da iyalinsa kayan abinci da kudi.

Bayan nan tawagar taje karamar hukumar Gaya inda ta gana da iyala Umar Mustapha wanda yake fama da rashin lafiya, inda a yanzu haka yana karbar magani a kasa mai tsarki, Alh. Laminu Rabi’u ya tabbabatarwa da iyalansa cewa da zarar ya dada samun lafiya za a dawo dashi gida Nigeria, sannan ya gabatar musu da kayan abinci da kudi.