Sarki Salman ya naɗa Abdul Rahman Al-Sudais a matsayin ministan kula da masallatan Haramin Makka da Madinah

0
310

Sarkin Salman na Saudiyya ya naɗa Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais a matsayin shugaban babban ofishin harkokin addini na Masallan Haramin Makka da Madina, wanda muƙamin ya ke daidai da minista.

Kazalika, Sarkin ya naɗa Ministan Hajji da Umrah, Dr. Tawfiq Al-Rabiah, a matsayin shugaban kwamitin daraktoci na babban ofishin kula da harkokin masallatan Haramin guda biyu.

An yi naɗe-naɗen ne a cikin wasu ƙudurori biyu na masarauta da Sarkin ya bayar biyo bayan matakin da Majalisar Ministocin ta ɗauka a jiya Talata na kafa babban ofishin da babbar hukuma a matsayin hukumomi biyu masu zaman kansu. Kuma dukkan ɓangarorin biyu za a danganta su da Sarkin.

Kafin sabon naɗin, Dr. Al-Sudais shi ne shugaban kula da harkokin masallatan biyu masu alfarma wanda daga bisani aka juya ta koma Babbar Hukumar kula da masallatan biyu.

Ayyukan kula da harkokin da suka shafi masallatan masu alfarma da kula da limamai da ladanai na masallatan da sauransu, su ne suka rataya a kan sabon shugabancin.

Yayin da kuma Babbar Hukumar ƙarƙashin jagorancin Al-Rabiah, za ta kasance mai cin gashin kanta kan sha’anin kuɗi da kuma gudanarwa.

Sauran ayyukan hukumar sun haɗa da hidima da sauran ayyukan bunƙasa Masallacin Ka’abah da ke Makka da Masallacin Annabi da ke Madin