Lautai Old Boys Association, LOBA, ƙungiyar tsoffin ɗalibai na Lautai Government Boys Secondary School, Gumel sun karrama shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbaffa.
Da ya ke jawabi a yayin taron, wanda ya gudana a hukumar alhazan a ranar Laraba, shugaban kungiyar tsofaffin daliban, Nafi’u Shu’aibu, ya ce suna godiya sosai ga Allah Madaukakin Sarki da ya baiwa Danbaffa damar zama shugaban hukumar.
Ya ce Danbaffa ya cancanci ya rike hukumar a karo na uku suna da kwarewar da ta aiki da kuma gaskiya da riƙon amana.
Malam Nafi’u Sha’aibu yace akwai wata magana da ta shahara da ke cewa “ladan aiki mai kyau ya fi aiki,” kuma mun yi imanin nadin da kuka yi ya tabbatar da wannan maganar a matsayin gaskiya, haka lamarin yake a cikin wannan yanayi.
Shugaban ya kara da cewa, ” Nadin Alhaji Laminu Rabi’u Danbaffa, I ko shakka babu aikin Allah Madaukakin Sarki ne domin tabbatar da sadaukarwar da ya ke yi da sadaukar da kai ga kasar sa ta haihuwa.
A nasa jawabin, Danbaffa, ya gode wa tsofaffin abokan karatun nasa bisa taya shi murna da suka yi tare da yin alkawarin kasancewa jakadan kungiyar tasu na gari
Danbaffa, ya kuma yi amfani da taron wajen sake godewa Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa sake bashi wannan dama da suka yi don ya hidimtawa bakin Allah
Daga nan sai yayi alkawarin sake bajiro da shirye-shirye da tsare-tsare da zasu kara bunkasa kula da jin dadin alhazan Jahar Kano.