Hajjin 2024: Ministan Hajji da Umrah na Saudi ya fara ziyarar aiki zuwa Pakistan da Bangladesh

0
116

Ministan harkokin Hajji da Umrah na Saudi Arebiya, Dr. Tawfiq Al-Rabiah ya fara ziyarar aiki zuwa kasashen Pakistan da Bangladesh.

Makasudin ziyarar ita ce domin haɗa gwiwa don ɓullo da sabbin dabaru na Hajji da Umrah da kuma yadda za a kara i ganta hidimomin mahajjata zuwa masallatan Harami masai tsarki guda biyu.

A yayin ziyarar, in ji jaridar SPA, Al-Rbiah, wanda shi ne shugaban kwamitin shirin “Hidima ga Baƙin Allah”, zai kuma gana da mahukunta daban-daban a kan bunƙasa harkokin Hajji da Umrah.

Hakazalika ziyarar za ta kara bunkasa alaƙar kasashen da Saudi Arabia ta hanyar addini da al’ada da za su yi daidai da shirin Saudiyya na Vision 2030.

Ziyarar, a cewar SPA ɓangare ne na ziyarce-ziyarxe da kasar ta fara tun 2022 da nufin sake kulla alaƙa don bunƙasa aikin Hajji da Umrah.