Jihar Edo ta fara karɓar kason farko na kuɗin Hajjin 2024

0
419

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Edo, Sheik Ibrahim Oyarekhua, ya bayyana cewa maniyyatan sun fara biyan kason farko na kuɗin aikin Hajjin badi a kasar Saudiyya.

Sheik Ibrahim wanda ya bayyana haka ga Daily Trust a jiya Litinin ya kuma bayyana cewa hukumar ta mayar da sama da Naira dubu 600,000 ga iyalan wani mahajjaci mai suna Momodu Alliakhu wanda ya rasu yana aikin Hajji a Makkah.

Ya ce, “Alhazai masu niyya sun fara saka kudi don aikin Hajjin badi.

” Babu mafi ƙarancin adadin; haka za su ci gaba da ajiyewa har zuwa lokacin da hukumar alhazai ta kasa ta bayyana cikakken adadin kudin da za a biya.

Duk da cewa NAHCON ba ta sanar da kudin aikin Hajji ba, ba ma tunanin zai gaza Naira miliyan 4 da abin da ke faruwa na canjin Dala ba. Kamar yadda kuka sani gwamnati ta cire tallafi kuma dala ta yi tsada.”

Ibrahim ya ce duk wanda ya ajiye sama da kudin da aka sanar za a mayar masa da rarar kudinsa yayin da wadanda suka ajiye kasa da haka za su cika.