Muna fatan alhazan Oyo su fara tashi a filin jirgin sama na Alakia a Hajjin baɗi- Gwamnati

0
273

Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana fatan ta na kammala aikin filin jirgin sama na Alakia domin alhazan jihar su fara tashi zuwa ƙasar Saudi Arebiya domin gudanar da aikin Hajji na 2024.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su kwantar da hankalinsu kan yadda ta ke kokarin gyaran fuska ga hukumar jin dadin Alhazai Musulmai ta jihar.

Tabbacin ya zo ne a wajen taron godiya ga sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Oyo, Sheik Hashim Abdulwahab Atere wanda aka gudanar a dakin taro na Oja’ba Multipurpose Hall, Ibadan a yau Alhamis.

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Raji Khaleel, ya fitar a yau Alhamis.

A jawabinsa na maraba, Turaki Adini na jihar Oyo, Mogaji Adanla Kareem ya yabawa gwamnatin gwamna Seyi Makinde kan yadda take baiwa al’ummar musulmi fifiko.

Mogaji Adanla a cikin sakonsa ya yi kira da a ba wa kowane musulmin jihar hadin kai domin bunkasa hukumar.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde wanda sabon shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Oyo ya wakilta, Sheik Hashim Abdukwahab Atere ya bayyana cewa gwamnati ta tsara shirye-shiryen baiwa hukumar wani sabon mataki da fatan za a dauka filin jirgin saman Alakia domin zuwa aikin Hajjin badi.

Tun da fari, Babban Limamin Jihar Oyo, Sheik Abubakry Agbotomokekere ya bayyana nadin a matsayin wata babbar kyauta ga daukacin al’ummar Musulmi domin bunkasa harkokin addini.

Taron ya samu halartar uwargidan PDP Patron a jihar Oyo, Misis Bosede Modinat Adedibu, Fmr. Kakakin PDP, Engr. Akeem Olatunji, Imamai, da sauransu.