Ƴan bindiga sun sace jami’in alhazai a Kano

0
184

Wasu yan bindiga sun yi awon-gaba da Sagiru Umar Kofa, jami’in alhazai na ƙaramar hukumar Bebeji a jihar Kano.

Hajj Reporters Hausa ta tattaro cewa ƴan bindiga sun kutsa kai cikin gidan Sagiru da tsakar da de, inda su ka yi wani gana da shi.

Sagiru dai shi ne hadimi na musamman ga Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Bebeji a Majalisar Wakilai.

Kawo yanzu dai yan bindigar ba su tuntubi iyalan Sagiru din ba.