Ma’aikatar harkokin Hajji ta hana zuwa masallacin Annabi da jaka

0
271

Kasar Saudiyya ta sanar da wasu dokoki ga masu ziyartar masallacin Annabi da ke Madina.

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta fitar da dokoki, wanda daga ciki har da dokar da ta hana shiga da jaka a wuraren da ake yin sallah a cikin masallacin.

Ka’idojin sun hana shiga da manyan jakankuna da akwatuna cikin harakar masallacin, kuma an hana shiga da kananan jakankuna zuwa wuraren sallah.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta shafintw na sada zumunta na yanar gizo ta ce: “Don tabbatar da ziyarar masallacin Annabi cikin aminci da tsari, muna rokon ku da ku bi ka’idoji, dangane da ajiyar kayanku.

“Ga kananan jakankuna da akwatuna, an haramta shigo da su wuraren da aka ware domin yin sallah. Da fatan za a yi amfani da lokokin da aka tanada a wajen masallacin don ajiye waɗannan jakankuna na ku.

“Kada a shigo da manyan jakankuna a cikin harabar masallacin ko kuma a ajiye su a farfajiyar waje da ke kusa, saboda akwai karancin waje a lokokin da aka tanada don ajiye irin waɗannan akwatuna,” in ji sanarwar.