NAHCON ta shawarci maniyyata aikin Hajjin baɗi da su ajiye Naira miliyan 4.5

0
511

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta shawarci ƴan Nijeriya da ke da niyyar zuwa aikin Hajji a shekara mai zuwa da su yi tanadin akalla Naira miliyan 4.5 kafin hukumar ta ƙayyade kudin aikin Hajjin.

Shugaban hukumar, Alh. Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan a jiya Talata yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar Hajji ta NAHCON da ke Abuja.

Yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai, shugaban na NAHCON ya ce tashin canjin dalar Amurka ne ya janyo tashin kuɗin aikin Hajjin.

Alhazan Najeriya sun biya kusan Naira miliyan 3 don aikin Hajjin bana, inda a lokacin an canjar da dala ne a kan Naira 416 a babban bankin Nijeriya.

Sai dai sauye-sauyen da aka samu a kasuwar musayar kudaden kasashen waje, a halin yanzu ya sanya ana canjin dala a kan Naira 750 zuwa N800.

A wani labarin kuma, daga yanzu mahukuntan kasar Saudiyya sun umurci ma’aikatar harkokin Hajji da ta dakatar da bayar da biza kwanaki 50 kafin Arafat, wanda hakan ya saɓawa tsohuwar al’adar bayar da bizar har zuwa daf da a fara ayyukan Hajji.