NAHCON ta buƙaci taimakon ƴan Kannywood wajen wayar wa da alhazai kai kan aikin Hajji

0
338

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya yi kira ga ƴan masana’antar fim ta Kannywood da su ci gaba da amfani da kafafen su wajen wayar da kan ‘yan Nijeriya musamman Alhazan Nijeriya ta hanyar fasaharsu.

Ya bayyana haka ne a jiya Alhamis, a lokacin da kungiyar Kannywood Action Forum, karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Kaka ta kai ziyarar ban girma ga hukumar NAHCON a shelkwatar ta da ke Abuja.

Shugaban ya bayyana imaninsa cewa tare da dimbin mabiyan Kannywood, musamman a Arewacin Najeriya, ayyukansu ko labaransu za su taimaka matuka wajen nuna kyakykyawan kimar kasar da kuma taimakawa wajen kawo canji ga al’umma.

Tun da fari, a nasa jawabin, jagoran tawagar Alhaji Ahmed Kaka ya taya hukumar murnar kammala aikin Hajjin 2023 cikin nasara duk da kalubalen da aka fuskanta.

Don haka ya yi kira da a hada kai a tsakanin kungiyoyin biyu musamman ta fannin wayar da kan alhazai da tsawaita amfani da kafafen sada zumunta na zamani.

Kungiyar ta kuma baiwa Alhaji Nura Hassan Yakasai, Kwamishinan PPMF a NAHCON da lambar yabo ta taimakon jin kai bisa gudunmawar da ya ke bayarwa wajen taimako ga marasa galihu a cikin al’umma.

Alhaji Yakasai, wanda ya bayyana jin dadinsa ga ƙungiyar, ya tabbatar musu da shirye-shiryen Hukumar na hada kai da su don cimma manufar NAHCON ta ci gaban aikin Hajji nan gaba.