Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta ce ta kafa wani kwamiti da zai nemo wani sabon kamfanin Mutawifs, da zai samar da ingantacciyar hidima ga alhazan Najeriya a lokacin aikin hajjin 2024.
Mutawifs kamfanoni ne na cikin gida a Saudi Arabiya waɗanda ke ba da ayyuka iri-iri ga mahajjata. Suna tsara zirga-zirga tsakanin tashoshin shiga da wurare masu tsarki, masaukai, ciyarwa da sauran ayyukan da mahajjata ke bukata.
Alhazan Najeriya sun koka kan hidimomi mara sa inganci da wasu kamfanonin Mutawwif a Saudiyya ke yi musu.
Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya ce an kafa wani kwamiti da zai samar da wasu kamfanoni da za a bi kafin aikin hajjin 2024.
Ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen taron lacca da lambar yabo na Hajj Reporters na 2023.
Ya ce an raba wuraren aikin hajji ga hukumomin jin dadin alhazai da hukumomin jiha domin shirye-shiryen aikin hajjin 2024 kan kari.