Bauchi ta sanar da Naira miliyan 3 a matsayin kashin farko na kuɗin aikin Hajjin badi

0
425

Jihar Bauchi ta bayyana Naira Miliyan 3 a matsayin kashin farko na kuɗin aikin hajjin 2024, inda ta bayyana ranar 1 ga Oktoba zuwa 31 ga Disamba na wannan shekarar don karbar kudaden ajiya daga hannun maniyyata.

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan aikin hajji a ofishin sa.

A sanarwar da Muhammad Sani Yunusa, jami’in yada labarai ya fitar, Hukumar Alhazai ta kasa wato NAHCON a baya ta sanar da miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiya na aikin Hajjin bana.

Inda ya kara da cewar jihar Bauchi ta zabi mafi karancin adadi ne bisa laakari da halinda da ake ciki na tattalin arziki a kasa.

A cewarsa maniyyata na da zabin biyan adadin da yafi miliyan 3 kafin sàmun sanarwar tartibin kudin aikin hajji daga hukumar alhazai ta kasa.

Ya kara bayyana cewar NAHCON ta ware gurbin kujerun aikin hajji dubu 3,364 ga Jihar Bauchi, inda ya kuma bada tabbacin fifita wadanda su ka ajiye kudin su a hukumar kuma basu sami damar zuwa aikin hajjin da ya wuce ba.

Imam Abdurrahman ya ci gaba da cewar hukumarsa ta sauya cibiyar biyan kudin ajiyan aikin hajji dake hedkwatar hukumar wato BS1 da tsarin adashen gata wato Hajji Savings Scheme, inda ya shawarci masu bukatar biyan kudin ajiyar da su garzaya Bankin Jaiz domin yin rijistar kansu a tsarin biyan Kudin ajiyan aikin hajjin su.