NAHCON ta nemi kamfanin Saudiyya ya maido da kuɗaɗen hidimomin da bai yi wa alhazan Nijeriya ba

0
315

Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, ta buƙaci kamfanin Mutawiff na Saudiyya da ya maido da kuɗaɗe na rashin aiwatar da wasu hidimomi da bai yi ba kwata-kwata ko kuma ya yi rabi-da-rabi ga alhazan Nijeriya.

NAHCON ta nemi maido da kuɗaɗen ne a wasiƙar da ta aike wa Ministan Hajji da Umara na Saudiyya, mai ɗauke da ƙorafin rashin samar da wadatattun tantuna ga alhazan Najeriya da ƙarancin abincin da alhazan suka fuskanta daga kamfanin Mutawiff wanda ke da alhakin yi wa ƙasashen Afirka waɗanda ba Larabawa hidima yayin Hajjin 2023.

Wasiƙar, wacce HAJJ REPORTERS ta samu kwafi, ta buƙaci Ministan Hajji da Ummara na Saudiyya da ya umarci Kamfanin Mutawiff da ya maido da kuɗaɗen da aka biya shi saboda rashin yi wa alhazan Najeriya hidima yadda ya kamata a Mina ‘, yayin Hajjin 2023.

A cewar wasiƙar, NAHCON ta tunatar da Ministan cewa yayin taron haɗin gwiwa na shirye-shiryen Hajjin 2023 da aka gudanar, kamfanin Mutawiff ya ba da tabbacin yi wa tawagar alhazan Najeriya hidima yadda ya kamata.

NAHCON ta ƙara da cewa, “abun babu daɗi sanar da kai cewa da yawan masu ruwa-da-tsaki sun bayyana kulawar da aka samu yayin Hajjin 2023 a matsayin mafi muni idan aka kwatanta da na shekarun baya.

“Hakan ya bayyana ne a lokacin da aka ga dubban alhazan Najeriya na rukunin tantuna (A,B,C & D) zube a rana babu mafaka, babu ruwa, babu abinci yayin zaman Mina da Arfa.”

Kazalika, wasiƙar ta nemi daga yanzu, Ministan ya bar Najeriya da ta kula da batun ciyar da alhazanta da kanta yayin Hajji.

“Ma’aikatar ta sakar wa Najeriya ragamar ciyar da alhazanta duba da yadda aka yi ta samun akasi daga ɓangaren kamfanin Mutawiff.

“Daga yanzu, ya zamana ana killace tantuna, sanya musu tayil da shimfiɗa kafet da kuma girke wadatattun jami’an tsaro domin hana wasu mahajjata yi musu kutse a masauki. Sannan a bayyana komai dalla-dalla don gudun rikitarwa,” in ji wasiƙar.

Bayan haka, NAHCON ta nusar da Ministan cewa, ƙarancin tantuna da aka fuskanta yayin Hajjin 2023, hakan ya faru ne saboda maimaita wa alhazan Najeriya wurin da aka ba su a Hajjin 2022 inda ake da alhazai 43,000.

A ƙarƙashin lura ta 2 (iii) da NAHCON ta yi kamar yadda yake ƙunshe cikin wasiƙar, hukumar ta ce, “Ƙarancin gado da aka yi fama da shi, hakan ya faru ne sakamakon adadin gadon da aka ware wa alhazai 43,000 a 2022 su aka sake ware wa alhazan Najeriya su 95,000 yayin Hajjin 2023.”

Idan dai za a iya tunawa, alhazan Najeriya sun yi ƙorafi kan rashin igancin hidima daga kamfanoni yayin Hajjin da ya gabata.

Bugu da ƙari, NAHCON ta nuna rashin jin daɗinta na maida ƙarin gurbin jigilar mahajjata da aka bai wa jiragen Najeriya. Tana mai cewa, tana fatan za a dubi lamarin domin hana aukuwar hakan a gaba.

”Bari in ƙara da cewa, Hukumar Hajji ta Najeriya ba ta ji daɗin yadda al’amura suka kasance ba yayin jigilar alhazai kashi na biyu bayan kammala Hajji inda aka hana jiragen Najeriya gurbin jigilar alhazai domin kwashe alhazansu zuwa gida a makon farko,” in ji wasiƙar.

Don haka hukumar ta nemi a bai wa jiragen Najeriya fifiko wajen ba su gurbin jigilar alhazai a makon farko da kammala aikin Hajji saboda yawan alhazan.