Hukumar alhazai ta Plateau ta buƙaci maniyyata su ajiye Naira miliyan 2 kuɗin aikin Hajjin 2024

0
285

Hukumar Alhazai ta Jihar Plateau ta shawarci maniyyatan da ke son zuwa aikin hajjin 2024 da su fara ajiye Naira miliyan 2 kuɗin aikin hajji.

Hukumar ta kuma bayyana cewa hukumar Alhazai ta kasa, NAHCON ta baiwa jihar kujerun Hajji guda 1,345.

Hukumar ta kuma ce za ta bada fifiko ga wadanda ba su samu zuwa Hajjin 2023 ba, tare da kujerun da NAHCON ta ware, inda ta yi kira da a yi gaggawar fara biyan kason farko na kuɗin.

Hajiya Aishatu Ibrahim Saleh, mukaddashiyar sakatariyar hukumar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar, Alhaji Sanusi Namu ya sanyawa hannu.

A kwanakin baya ne NAHCON ta ware wa jihar Plateau kujerun aikin hajji 1,345 kuma za’a baiwa wadanda basu samu zuwa aikin hajjin 2023 ba fifiko.

Don haka ana kira ga dukkan maniyyata a kan lokaci domin duk maniyyatan za a yi musu magani da farko.

Sanarwar ta kuma shawarci wadanda ke da ajiya a hukumar kuma ba su yi aikin hajjin 2023 ba, da su zo hukumar domin samun ma’aikata domin su cika kudadensu.