Kuɗin Hajjn 2024: Ku fara ajiye Naira miliyan 3, gwamnatin Katsina ta fadawa maniyyata

0
343

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda, ya amince da fara rijistar maniyyata aikin hajjin 2024 da kuma karbar kashin farko na kuɗin daga maniyyatan jihar.

Babban Daraktan Hukumar Alhazai ta Jihar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ofishinsa a jiya Alhamis.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar, Badaru Bello Karofi ya fitar, Kuki ya kuma ce wadanda ke da niyyar zuwa aikin Hajji na badi za su fara ajiye ₦3,000,000,00.

“Sai dai ana sa ran nan da watan Disambar 2023 dukkan maniyyatan da suka yi rijista za su iya cika kuɗin ajiyar ta su zuwa ₦4.5m kafin hukumar NAHCON ta sanar da fara biyan kudin aikin Hajji na karshe,” inji shi.

Alhaji Kuki, ya shawarci maniyyatan da su biya kuɗin ta hanyar daftarin banki, amma ta asusun hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina, inda ya kara da cewa za a gudanar da aikin rajistar ne a dukkan ofisoshin shiyya bakwai na hukumar da ke Katsina, Funtua, Malumfashi, Dutsinma, Kankia, Daura da Mani.

Daraktan ya ce za a yi rajistar ne bisa ga tsarin wanda ya fara biya.

Hakazalika Kuki ya kuma bayyana cewa hukumar ta karbi kujerun aikin Hajjin 2024 dubu 4,513 daga hukumar alhazai ta kasa, NAHCON.