Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta makonni uku su ka rage mata domin tattaunawa da kamfanonin yi wa alhazai hidima a kasar Saudiyya, inda ta bukaci maniyyata da su biya Naira miliyan 4.5 na kuɗin ajiya kafin lokacin.
Mataimakiyar Daraktar Hulda da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara a cikin wata sanarwa a yau Alhamis, ta ce Saudiyya ta sanya ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023 don kammala taron share-fage da masu da kamfanonin yi wa alhazai hidima, inda ta ce kafin nan ya kamata hukumar ta yi kiyasin adadin maniyyata aikin Hajji domin samun damar tattaunawa wajen fitar da da tabbataccen kuɗin Hajjin bana.
Sanda ta ce shirye-shiryen aikin hajjin 2024 da wuri-wuri ne ya sanya NAHCON da kuma Muryar Shugabannin Hukumomin Alhazai na Jihohi ne ya sanya aka tsayar da Naira miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiya na Hajjin bana.
“Hikimar da ke tattare da wannan mafi ƙarancin ajiya ta ta’allaka ne akan dalilai uku. Na farko, shi ne jihohi da hukumominsu su yi kiyasin adadin maniyyata nawa ne za su cancanci a kidaya su a matsayin mahajjata akalla nan da 4 ga Nuwamba, 2023, lokacin da Saudiyya ta sanya hukumar ta kammala taron share fage da masu ba da hidima. Sanin kiyasin adadin maniyyatan da suka cancanta na daga cikin filaye da za su jagoranci tarurrukan share fage. Wannan wa’adin Saudiyya ya kusa makonni uku kenan.”
Ta kara da cewa an amince da adadin kudin ne domin baiwa mahajjata damar biyan sauran kudaden cikin sauki idan aka bayyana tabbataccen kudin Hajji na karshe.