Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Alhaji Jalal Ahmad Arabi a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) na tsawon shekaru hudu (4) a matakin farko.
A sanarwar da mai bawa Shugaban kasa shawara kan harkokin kafafen yada labarai da hulda da jama’a,Chief Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu, ya ce Shugaban ya umarci shugaban hukumar mai barin gado kuma babban jami’in hukumar Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da ya ci gaba da hutun watanni 3 kafin ya yi ritaya kamar yadda dokar ma’aikatan gwamnati (PSR) 120243 ta tanadar daga ranar 18 ga Oktoba, 2023, wanda ya kai ga a ƙarshe ya yi ritaya daga aiki a ranar 17 ga Janairu, 2023.
Sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Alhaji Jalal Ahmad Arabi, zai fara aiki a ranar 18 ga Oktoba, 2023, kuma zai ci gaba da yin aiki mai inganci har na tsawon shekaru hudu, daga farawa. a ranar 17 ga Janairu, 2023.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kuma amince da rusa hukumar ta NAHCON.
Shugaban ya yi fatan sabbin shugabannin hukumar ta NAHCON za su yi aiki cikin tsoron Allah tare da kiyaye ka’idojin aiki kamar yadda Alkur’ani mai girma ya fada.