Jalal Arabi, sabon shugaban hukumar alhazai ta ƙasa, NAHCON, ya yi alkawarin mayar da hukumar zuwa mahimmin ajandar sabunta fata na shugaban Bola Tinubu.
Mista Arabi ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake jawabi ga mahukunta da ma’aikatan hukumar a lokacin da ya fara aiki a shelkwatar hukumar a yau Laraba a Abuja.
Ya ce: “Lokaci ya yi da za mu buɗe sabon shafi. Ajandar Sabunta Fata na gaske ne. Ba na buƙatar yin wani bincike. Da gaske ne.
“Dukkanku kun sani kuma na yi imani dukkan ku za ku iya tabbatar da cewa lokacin da Shugaba Bola Tinubu ke yawo da wasu daga cikinmu abin farin ciki ne mu zagaya da shi da kuma wadanda suka yi magana a madadinmu.
“Akwai alkawari kuma hakika an yi alkawari a wancan lokacin cewa abubuwa za su yi kyau kuma ba shakka a yanayi dole ne a sami canji.
“Kuma dole ne canji ya magance abubuwan da suka lalace amma tabbas kuna son sake fasali, kuma ku ci gaba kuma na yi imani ina bukatar hadin kan ku a wannan bangaren.”
Mista Arabi wanda ya nemi hadin kan ma’aikata da shugabannin hukumar, ya shawarci wadanda
ba su shirya sadaukarwa don samun nasarar hukumar ba da su bar aiki.