Sabon shugaban Hukumar aikin Hajji ya Ziyarar ci Sheikh Bala Lau

0
185

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Sabon Shugaban hukumar aikin Hajji na kasar Naijeriya (NAHCON) Alhaji Jalal Ahmad Arabi, ya Ziyarar ci shugaban kungiyar wa’azi na Musulunci na JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau a gidansa dake Birnin tarayya Abuja.

Jalal Arabi ya Kai wannan ziyara ce domin fatan alheri, tare da neman shawarwari na yadda zai gudanar da sabon aikin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dora masa na jagorantar aikin Hajji a Naijeriya zuwa kasar Saudi Arabia.

Sheikh Bala Lau ya nuna yaji dadin wannan ziyara, inda yaja hankalinsa wajen aiki tukuru domin samun nasara Mai nagarta.

Jalal Arabi ya Samu babban Sakataren Kungiyar JIBWIS Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe a tare da Shugaban.

Kazalika Tsohon Shugaban Hukumar alhazai na kasa, Barista Abdullahi Mukhtar na daya daga cikin wadanda suka raka sabon shugaban zuwa wannan ziyara Mai aminci.

SOURCE: JIBWIS NIGERIA