Umrah: Wata ƴar Sudan ta haihu a haramin Makkah

0
312

Wata alhajiyar Umrah yar ƙasar Sudan ta haihu yayin da table gudanar da ibada a babban masallacin Harami a Makkah.

Tawagar motocin daukar marasa lafiya na kungiyar agaji ta Red Crescent ta Saudiyya da ke Makkah ne su ka kula da matar, wacce naƙuda ta riske ta, ta kuma haifi santalelen jaririnta, yayin da ta ke gudanar da ibada s Harami.

Daraktan kungiyar agaji ta Red Crescent, reshen Makkah, Dr. Mustafa Baljoun ya bayyana cewa, hukumar gudanarwar ƙungiyar ta samu rahoton ne a yau Litinin da karfe 12:05 na safe.

Rahoton ya bayyana cewa wata mata tana fama da ciwon ciki a farfajiyar Masallacin Harami daura da Otel din Al-Tawhid.

Da isar tawagar likitocin, a cewar sa, sai su ka gano cewa matar na naƙuda ne kuma ta na daf da haihuwa.

Ya ce nan da nan mahaifar matar ta buɗe, ruwa ya ɓalle, sai ga kan jaririn ya riga ya fito. Ya ce, nan take tawagar motocin daukar marasa lafiya suka taimaka mata bisa ka’ida a irin wannan yanayi.

Dokta Baljoun ya nuna cewa matar ta yi nasarar haihuwar jaririn, inda nan take aka wuce da ita da jaririn zuwa babban asibitin Ajyad, inda aka tabbatar da cewa dukkansu suna cikin koshin lafiya.

Ya jaddada mahimmancin kiran agajin motar asibiti lokacin da buƙatar gaggawa ta tashi, ta hanyar kiran 997.