Wani mai kamfanin sufurin ƙasashen waje ya fadi ya rasu a ofishin NAHCON

0
215

Manajan Darakta na wani kamfanin sufurin ƙasashen waje, Danlami Umar ya yanke jiki ya fadi ya rasu a lokacin da ya ke yin rijistar halartar wani taro da mukaddashin shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON.

Marigayi Umar shi ne mai kamfanin Hasha Travels kuma yana cikin tawagar kungiyar masu jigilar aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON).

Kakakin AHUON, Alh Nasiru Chamo wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga HAJJ REPORTERS, ya ce marigayi Umar “ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ya ke sanya hannu a littafin rajista na masu ziyara, inda ya rasu a hanyar zuwa Asibiti”.

Har ila yau, wata sanarwa da kakakin hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki ya fitar ta ce mukaddashin Shugaban hukumar NAHCON, Malam Jalal Arabi ya yi wa iyalan Danlami Umar ta’aziya.

Shugaban, a cewar sanarwar, ya bayyana mutuwa a matsayin abu na babu makawa.

“Mutuwa babu makawa. A matsayinmu na Musulmai imaninmu shine cewa ba za’a iya ƙara dakika ɗaya ba idan lokaci ya yi.

” Zuciyarmu tana tare da iyalansa, abokansa da abokan zamansa a wannan lokaci. Allah Ta’ala Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma baiwa ‘yan uwa kwarin guiwar jure rashin”.