Hukumomi sun fara rijistar masaukan alhazai a Madina

0
206

Hukumomi a birnin Madina mai tsarki na kasar Saudiyya sun sanar da fara rijistar samar da masaukai ga alhazai, a wani mataki na shirye-shiryen hajjin shekara mai zuwa.

Magajin Gari a Madina, ya yi kira ga masu hidimomi na musamman ga alhazai ɓangaren masauki da abinci da su yi amfani da takardun da ake bukata ta adireshin yanar gizo: investment.amana-md.gov.sa/HajEasha a kan dandalin ma’aikatar Hajji.

Har yanzu dai ba a bayyana wa’adin ba rufe yin rijistar ba, inda a watan Yuni ne za a fara aikin Hajji na shekara mai zuwa.

A wani bangare na shirye-shiryen farko na lokacin aikin hajji, a watan Yuli hukumomin Madina sun bude rajistar kama masaukan maniyyata a birnin.

Ana yin rajistar ne har zuwa karshen watan Rajab, wata na takwas a kalandar Musulunci.