Hajjin 2024: Za mu ciyar da alhazan Nijeriya da irin abincinsu na gargajiya — Kamfanin Mutawifs

0
478

Kamfanin Saudiyya mai yi wa ƙasashen Afirka da ba Larabawa ba hidima a lokacin Hajji, Mutawifs, ya yi alƙawarin samar da abincin gargajiya ga alhazan Najeriya yayin aikin Hajjin 2024.

Kazalika, kamfanin ya sha alwashin yin aiki ba dare, ba rana domin yi wa mahajjatan Najeriya hidima yadda ya kamata da zummar cika alkawarin da ya ɗauka na inganta harkokinsa, biyo bayan kokawa da hukumomin Najeriya suka yi na rashin samun kulawar da ta dace daga gare shi yayin Hajjin 2023.

Babban jami’i a kamfanin, Dr. Ahmad Abbas Sindi, shi ne ya bayyana a wata ganawa da suka yi da muƙaddashin Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Malam Jalal Ahmed Arabi, a babban ofishin hukumar da ke Abuja a jiya Lahadi..

Sanarwar da NAHCON ta fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai, Mousa Ubandawaki, ta nuna cewa, Sindi ya bayyana haka ne don amincewa da buƙatar Arabi na kamfanin ya inganta ayyukansa yayin Hajjin 2024.

“A martaninsa, Shugaban Mutawif ya bada tabbacin mahajjatan Najeriya za su samu kyakkyawar kula yayin Hajjin 2024 mai zuwa,” in ji kamfanin

Shugaban kamfanin ya ƙara da cewa, sun bada himma wajen bunƙasa hidima ga mahajjata a Mina da Arfa, tare da bayyana irin canje-canjen da suka yi a ɓangarori daban-daban domin cimma nasara a ayyukansu.

Sanarwar ta ce, “Haka nan, ya taɓo batun kyakkyawan tanadin da suka yi don kyautata makewayi da kuma yadda za a rarraba su. Sai kuma batun cima, a nan ma ya ce an samar da ingantaccen tsari don tabbatar da mahajjatan Najeriya na samun abin kaiwa bakin salati a kan lokaci.

“Mun bai wa masu sayar da kayayyaki aikin sayo kayan abinci daga Najeriya, sannan an ɗauki hayar masu girki ‘yan Najeriya don samar da abinci irin na ƙasar.

“A shirye muke wajen aiwatar da sabbin tsare-tsaren namu da kuma tabbatar da abinci na isa ga mahajjatan Najeriya a tantunansu a kan kari. Mun sha alwashin da yardar Allah, za a fuskanci kyakkyawan aikin Hajji a 2024.

“Dangane da jigilar mahajjata kuwa, ya ce akwai shirin da aka yi don yauƙaƙa zirga-zirgar motoci tsakanin Mina, Muzdalifa, Arfa da Makkah domin hana aukuwar matsalar da aka fuskanta a baya. Shugaban ya bada tabbacin motocin jigilar za su riƙa zirga-zirga ne na sa’o’i 24 domin cimma buƙatun mahajjata.”

Sindi ya kuma yi alƙawarin za su yi dukkan mai yiwuwa wajen maido da kuɗaɗen aikin da ba su yi ba yayin Hajjin 2023.

Tun da fari, Shugaban NAHCON ya roƙi kamfanin da ya kyautata ayyukansa ga mahajjatan Najeriya a Masha’ir yayin Hajjin baɗi.

Haka nan, ya nuna muhimmancin haɗa kai a yi aiki tare don samar da dauwamammiyar mafita dangane da matsalolin da aka fuskanta yayin Hajjin 2023.