Gwamna Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina a jiya Laraba ya amince da nadin Hon. Yunusa Abdullahi Dankama da Alhaji Kabir Bature a matsayin babban darakta da kuma shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina.
Haka kuma gwamnan ya naɗa wasu mutane 17 a matsayin mambobin kwamitin gudanarwar hukumar.
A wata sanarwa da Ibrahim Kaula Mohammed, wanda shi ne babban sakataren yada labarai, CPS, ga Radda ya fitar, ya ce dukkan nade-naden za su fara aiki ne na gaggawa.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da: Dr. Badiya Hassan Mashi, Alhaji Bala Abubakar Daura, Hajiya Rukayya Umar Gojo-Gojo, Hajiya Safara’u Masari, Hajiya Bilkisu Abdullahi, Sheik Dr. Munnir Jafar, Sheik Dr. Saifullahi Yakubu Musa, Sheik Nasiru. Abdurhamn, Malam Aliyu Umar Imam, Alhaji Saminu Suleiman, Alhaji Abdullahi Abubakar Darma, Alhaji Bishir Dangambo, Alhaji Usman Umar Mani, Alhaji Inusa Tijjani Canada, Allarama Kafin-soli, Alarama Rufa’i Nasir da Alhaji Abdullahi Fikira.
Gwamna Radda ya buƙaci sabon kwamitin zartaswa na hukumar da kuma Shugaban nata tare da sauran mambobi su 17 da su jajirce da rikon amana wajen yi wa al’ummar jihar hidima da gwamnatin jihar baki daya.
“Mai martaba, Mallam Dikko Radda, ya kuma yi kira gare su da su himmatu wajen ganin hukumar ta yi tasiri wajen daidaita dukkan ayyukan da suka shafi aikin hajji,” in ji wani bangare na sanarwar da CPS ga Radda ya fitar.